ABNA24 : Tashar talabijin ta Al-Masirah ta nakalto Abdulkadir Murtala shugaban kwamitin fursinonin yaki na kasar ya na fadar haka.
Almurtala ya bayyana a yau Lahadi kan cewa an yi musayar fursinoni 5 na gwamnati da kungiyoyin sa kai na kasar ta Yemen da wasu na wancan bangaren.
Kafin haka dai a ranakun 15 da 16 na watan Octoban da ya gabata an yi musayar fursinoni 1,016 tsakanin bangarorin biyu. Sannan an yi musayar ne karkashin kula na majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar RED CROSS.
Wannan dai shi ne musayar fursinoni mafi girma tsakanin bangarorin biyu tun farkon yakin a shekara ta 2015-(19)
342/